1 Kings 18:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ahab ya ce wa Obadiya, “Ka ratsa ƙasar zuwa dukan maɓulɓulai da fadamu. Mai yiwuwa ka sami ciyawa mu ba dawakai da alfadarai don su rayu, don kada mu kashe dabbobinmu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَهَبْ يَثٜىٰ وَ عُواْبَدِيَ «تَڢِے كُواْعِنَ ثِكِنْ ڧَسَرْ، كَبِے تَدُكَنْ مَٻُٻُّغَرْ ضُوَ دَ رَاڢُڢُّكَ؞ وَتَڧِيلَ ذَامُ سَامِ ثِيَوَ دُواْمِنْ مُثٜىٰثِ دَوَكِ دَ جَاكُنَنْ دُواْكِ دَغَ مُتُوَ، كَدَ مُرَسَ دَبُّواْبِنْمُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Ahab ya ce wa Obadiya, “Ka tafi ko'ina a ƙasar duk inda maɓuɓɓugan ruwa suke, da inda fadamu suke duka, watakila ma sami ciyawa mu ceci rayukan dawakai da alfadarai, don kada mu rasa waɗansu.”