1 Kings 19:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Elisha ya bar shanun, ya ruga ya bi Iliya. Ya ce, “Bari in sumbace mahaifina da mahaifiyata, in yi musu bankwana, sa’an nan in zo in bi ka.” Iliya ya ce, “Koma! Me na yi maka?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَلْيَسَعَ يَبَرْ شَانُنْ نُواْمَنْسَ يَبِے إِلْيَاسُ عَبَايَ دَ غُدُ يَثٜىٰ «بَرِ إِنْ كُواْمَ إِنْيِ وَبَابَنَ دَ مَامَاتَ سُمْبَرْ بَنْ ݣُونَ، سَعَنً إِنْ كُواْمَ إِنْ عَيْكَ؞» إِلْيَاسُ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «كَتَڢِے، أَيْ مٜىٰنَيِمَكَ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya bar shanun noma, ya sheƙa gun Iliya, ya ce, “Bari in sumbaci mahaifina da mahaifiyata, in yi bankwana da su, sa'an nan in zo in bi ka.” Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Koma, me na yi maka?”