1 Kings 2:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki Solomon ya amsa wa mahaifiyarsa ya ce, “Me ya sa kika roƙar wa Adoniya Abishag mutuniyar Shunam kawai? Ki ma sa a ba shi mulkin mana. Ai, shi yayana ne. I, ki roƙa dominsa, da domin Abiyatar firist, da kuma domin Yowab ɗan Zeruhiya mana!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُلَيْمَٰنُ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «دُوانْمٜىٰ ذَاكِ ضُواْڧَاوَ أَدُواْنِيَ أَبِشَغْ؟ بَڠُومَّ كَوَيْ كِضُواْڧَا مَسَ مُلْكٍ بَ؟ دَيَكٜىٰ مَا شِ یَیَنَ نٜىٰ، كُمَ أَبِيَتَرْ ڢِرِسْتِ دَ يُواْوَبْ طَنْ ظٜىٰرُوِيَ سُنَ غُواْيُوانْ بَايَنْسَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai sarki Sulemanu ya amsa wa tsohuwarsa, ya ce, “Don me kika roƙar wa Adonija Abishag? Ki roƙar masa sarautar mana, gama shi wana ne, Abiyata, firist kuma, da Yowab ɗan Zeruya suna goyon bayansa.”