1 Kings 2:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yanzu kuwa, muddin Ubangiji yana a raye, shi wanda ya kafa ni sosai a kan kujerar sarautar mahaifina Dawuda, ya kuma kafa mini mulki kamar yadda ya yi alkawari; za a kashe Adoniya yau!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ يَا تَبَّتَرْ دَنِے يَاكُمَ سَا نِے عَكَنْ كُجٜىٰرَرْ مُلْكٍ بَابَنَ دَاوُدَ، يَكُمَ كَڢَ ظُرِيَاتَ تَذَمَ غِدَنْ مُلْكِ؞ نَا ضَنْڟٜىٰ دَ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ مَيْ رَيْ، سَيْ أَدُواْنِيَ يَمُتُ يَوْ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya kafa ni sosai a gadon sarautar tsohona, Dawuda, ya kuma cika alkawarinsa, ya ba ni mulki da zuriyata. Na rantse za a kashe Adonija yau.”