1 Kings 2:30 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Benahiya ya shiga tentin Ubangiji ya ce wa Yowab, “Sarki ya ce, ‘Ka fita!’ ” Amma Yowab ya amsa ya ce, “A’a, a nan zan mutu.” Sai Benahiya ya ce wa sarki, “Ga yadda Yowab ya amsa mini.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بٜىٰنَيَ يَتَڢِے وُرِنْ تٜىٰنْتِنْ يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ «سَرْكِے يَثٜىٰ كَڢِتُواْ؞» يُواْوَبْ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «أَعَ، نَنْ ذَنْ مُتُ؞» سَيْ بٜىٰنَيَ يَكُواْمَ وُرِنْ سَرْكِے يَڢَطَا مَسَ أَبِنْدَ يُواْوَبْ يَثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Benaiya kuwa ya tafi alfarwa ta Ubangiji, ya ce masa, “Sarki ya ce ka fito.” Amma Yowab ya ce, “A'a, a nan zan mutu.” Benaiya kuma ya je ya faɗa wa sarki abin da Yowab ya ce.