1 Kings 2:32 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji zai sāka masa saboda jinin da ya zubar, domin ba da sanin mahaifina Dawuda ne ya fāɗa wa mutum biyun nan da takobi ba. Dukansu biyu, Abner ɗan Ner, shugaban mayaƙan Isra’ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban mayaƙan Yahuda, mutane ne mafi kyau da kuma mafi adalci fiye da shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَهَكَ يَهْوٜىٰهْ ذَيْ رَامَ عَكَنْسَ أَلْحَكِنْ جِنِنْ وَطَنْدَ يَكَشٜىٰ بَاتَرٜىٰدَ سَنِنْ بَابَنَ دَاوُدَ بَ؞ يَكَشٜىٰ مُتَنٜىٰ بِيُ دَ تَكُواْبِے، وَتُواْ أَبْنٜىٰرْ طَنْ نٜىٰرْ، شُوغَبَنْ سُواْجُواْجِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ أَمَسَ طَنْ يٜىٰتٜىٰرْ، شُوغَبَنْ سُواْجُواْجِنْ يَهُودَ، وَطَنْدَ سُكَ ڢِيشِ أَدَلْثِے دَ أَلْحٜىٰرِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji zai ɗora masa alhakin mugayen ayyukansa, gama ya kashe mutum biyu ba da sanin tsohona Dawuda ba, waɗanda kuma suka fi shi adalci, wato Abner ɗan Ner, shugaban sojojin Isra'ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban sojojin Yahuza.