1 Kings 2:36 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan sarki ya aika aka kawo Shimeyi, ya kuma ce masa, “Ka gina wa kanka gida a nan a Urushalima, ka zauna a ciki, kada ka kuskura ka tafi wani wuri.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے يَعَيْكَ عَكَ كِرَا شِمٜىٰيِ يَثٜىٰ مَسَ «كَغِنَ وَكَنْكَ غِدَا أَنَنْ عُرُوشَلِيمَ، كَذَوْنَ عَثِكِ؞ كَدَ كَڢِتَ دَغَ بِرْنِنْ ذُوَا وَنِ وُرِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai kuma sarki ya aika a kirawo Shimai. Sa'an nan ya ce masa, “Ka gina wa kanka gida a Urushalima, ka zauna a nan, kada ka fita ko kaɗan zuwa wani wuri.