1 Kings 2:38 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shimeyi ya amsa wa sarki ya ce, “Abin da ka faɗa yana da kyau. Bawanka zai yi kamar yadda ranka yă daɗe sarki, ya faɗa.” Shimeyi kuwa ya yi zama a Urushalima na dogon lokaci.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
شِمٜىٰيِ يَأَمْسَ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، مَغَنَرْدَ كَيِ دَيْدَيْنٜىٰ، بَاوَنْكَ ذَيْ يِهَكَ؞» سَيْ شِمٜىٰيِ يَذَوْنَ أَ عُرُوشَلِيمَ ݣُونَكِے دَيَوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Shimai kuwa ya ce wa sarki, “Abin da ka faɗa daidai ne, abin da ka ce in yi, zan yi, ranka ya daɗe.” Sai Shimai ya zauna a Urushalima kwanaki da yawa.