1 Kings 2:46 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai sarki ya umarci Benahiya ɗan Yehohiyada, yă fita, yă bugi Shimeyi, yă kashe shi. Ya kuwa kashe shi. Mulki kuwa ya kahu sosai a hannun Solomon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً سَرْكِے سُلَيْمَٰنُ يَعُمَرْثِ بٜىٰنَيَ طَنْ يٜىٰهُواْيِدَ يَتَڢِے يَكَشٜىٰ شِمٜىٰيِ؞ سَيْيَتَڢِے يَكَشٜىٰشِ؞ أَوَنَّنْ لُواْكَثِ كُوَ مُلْكٍ يَكَڢُ دَݣَوْ أَ حَنُّنْ سُلَيْمَٰنُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan sarki ya umarci Benaiya ɗan Yehoyada, ya tafi, ya kashe Shimai. Yanzu sarauta ta tabbata a hannun Sulemanu.