1 Kings 2:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ka tuna, akwai kuma Shimeyi ɗan Gera, mutumin Benyamin daga Bahurim, wanda ya yi ta yin mini muguwar la’ana a ranar da na tafi Mahanayim. Sa’ad da ya gangara ya same ni a Urdun, na rantse masa da sunan Ubangiji na ce, ‘Ba zan kashe ka da takobi ba.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«أَݣَويْ كُمَ شِمٜىٰيِ طَنْ غٜىٰرَ مُتُمِنْ بِلِيَامِنُ دَغَ بَهُرِمْ؞ يَظَظْذَغٜىٰنِ سُواْسَيْ رَانَرْدَ نَتَڢِے مَهَنَيِمْ؞ عَمَّا دَ يَڢِتُواْ دُواْمِنْ يَتَرْيٜىٰنِ عَبَاكِنْ كُواْغِنْ يُواْدَنْ، نَا ضَنْڟٜىٰ مَسَ دَ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ ثٜىٰوَ بَذَنْ كَشٜىٰشِيبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ga kuma Shimai ɗan Gera, daga garin Bahurim ta Biliyaminu. Shi ne ya yi mini mugun zagi sa'ad da na tafi Mahanayim, amma sa'ad da ya zo taryata a Urdun, sai na rantse masa da Ubangiji, na ce ba zan kashe shi ba.