1 Kings 20:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ben-Hadad sarkin Aram kuwa ya tattara mayaƙansa gaba ɗaya. Sarakuna talatin da biyu suka tafi tare da shi haɗe da dawakansu da kekunan yaƙinsu. Ya haura ya yi wa Samariya kwanto, ya kuma yaƙe ta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے بٜىٰنْهَدَدْ نَ سُورِيَ يَتَتَّارَ سُواْجُواْجِنْسَ دَ سَرَاكُنَ تَلَاتِنْ دَ بِيُ، تَرٜىٰدَ دَوَكِنْسُ دَ كُمَ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْسُ؞ سُكَ تَڢِے سُكَ كٜىٰوَيٜىٰ سَمَرِيَ بَبَّنْ بِرْنِنْ ڧَسَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ، دُواْمِنْ سُڢَاطَ مَتَ دَ يَاڧِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ben-hadad Sarkin Suriya kuwa ya tara dukan sojojinsa. Sarakuna talatin da biyu kuma suna tare da shi, da dawakai, da karusai. Ya haura ya kai wa Samariya yaƙi. Ya kuwa yi yaƙi da ita.