1 Kings 20:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ben-Hadad ya ji wannan saƙo yayinda shi da sarakunan suke sha a cikin tentunansu, sai ya umarce mutanensa, ya ce, “Ku shirya don yaƙi.” Saboda haka suka shirya don su yaƙi birnin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بٜىٰنْهَدَدْ يَكَرْٻِ أَمْسَرْ وَنَّنْ سَڧُواْ سَعَدَّ شِے دَ سَوْرَنْ سَرَاكُنَنْ سُكٜىٰ شَيٜىٰ شَيٜىٰ عَثِكِنْ تٜىٰنْتِنْسُ؞ سَيْيَثٜىٰ وَسُواْجُواْجِنْسَ «كُشِرْيَ كُڢَارَ يَاڧِ؞» سَيْ سُكَ طَوْكِ مَتَاكَنْ شِغَ بِرْنِنْ دَ يَاڧِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Ben-hadad ya ji wannan saƙo sa'ad da yake sha tare da sarakuna a sansani, sai ya ce wa mutanensa, “Kowa ya tsaya a wurinsa.” Sai kowa ya tsaya a wurinsa don yin yaƙi da birnin.