1 Kings 20:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ana cikin haka sai wani annabi ya zo wurin Ahab sarkin Isra’ila ya sanar masa cewa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka ga wannan ɗumbun mayaƙa? Zan ba da su cikin hannunka a yau, sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ وَنِ أَنَّبِے يَذُواْ وُرِنْ سَرْكِے أَهَبْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ يَثٜىٰ مَسَ «إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ ، ‹كَغَا بَبَّنْ تَارُوانْ سُواْجُواْجِنَّنْ؟ لَلَّيْ ذَنْسَا كَيِ نَصَرَا عَكَنْسُ يَوْ! سَعَنً ذَاكَ سَنِ ثٜىٰوَ نِنٜىٰ يَهْوٜىٰهْ ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba da jimawa ba, sai ga annabi ya zo wurin sarki Ahab na Isra'ila, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Ka ga wannan babban taron sojoji? Zan ba da su a hannunka yau, za ka kuwa sani ni ne Ubangiji.’ ”