1 Kings 20:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka yi wannan. Ka cire dukan sarakuna daga matsayinsu ka sa waɗansu shugabanni a maimakonsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا أَبِنْدَ ذَاكَيِ؞ كَثَنْجَ سَرَاكُنَنَّنْ تَلَاتِنْ دَ بِيُ دَغَ مَڟَيِنْسُ، كَسَا شُوغَبَنِّنْ سُواْجُواْجِ أَمَيْمَكُوانْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yanzu abin da za ka yi ke nan, sai ka fitar da sarakuna daga matsayinsu, ka sa shugabannin sojoji maimakonsu.