1 Kings 20:27 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da aka tattara Isra’ilawa, aka kuma ba su guzuri, sai suka taka suka fita don su sadu da Arameyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani ɗaura da su kamar ƙananan garkuna biyu na awaki, yayinda Arameyawa suka rufe dukan jejin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَ تَتَّارَ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا عَكَبَاسُ كَايَنْ يَاڧِ، سُكَ ڢِتَ سُكَ ڢُسْكَنْثِ سُورِيَاوَنْ؞ إِسْرَٰٓءِيلَاوَنْ سُكَ تَتَّارُ كَمَرْ یَنْ غَرْكُنَ بِيُ نَأَوَكِ، عَمَّا سُرِيَاوَا سُكَ بَظُو سُكَ ثِكَ كُواْعِنَ أَ ڢِيلِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Aka tara mutanen Isra'ila, aka ba su guzuri, suka tafi, su yi yaƙi da Suriyawa. Isra'ilawa suka kafa sansani a gabansu kamar 'yan garkuna biyu na awaki, amma Suriyawa suka cika ƙasar.