1 Kings 20:29 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kwana bakwai suka yi sansani ɗaura da juna, a rana ta bakwai sai yaƙi ya haɗu. Isra’ilawa suka kashe sojojin kafa na Arameyawa dubu ɗari a rana ɗaya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَيِ ݣُونَكِے بَݣَويْ إِسْرَٰٓءِيلَاوَنْ دَ سُرِيَاوَنْ سُنَ ذَمَ أَ سَنْسَنِنْ يَاڧِنْسُ سُنَ ڢُسْكَنْتَرْ جُونَ؞ أَ رَانَ تَبَݣَويْ عَكَ شِغَ يَاڧِ، إِسْرَٰٓءِيلَاوَا سُكَ كَكَّشٜىٰ سُواْجُواْجِنْ سُورِيَ دُبُو طَرِے أَ رَانَ طَيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka kafa sansani daura da juna kwana bakwai. A rana ta bakwai ɗin, suka kama yaƙi. Isra'ilawa suka kashe Suriyawa mutum dubu ɗari (100,000) a rana ɗaya.