1 Kings 20:32 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saye da tufafin makoki kewaye a gindinsu, da kuma igiyoyi kewaye da kawunansu, suka tafi wurin sarkin Isra’ila, suka ce, “Bawanka Ben-Hadad ya ce, ‘Ina roƙonka bari in rayu.’ ” Sarki ya amsa, “Har yanzu yana da rai? Shi ɗan’uwana ne.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَسَا رِيغُنَنْ نُونَ بَڧِنْ ثِكِ، سُكَ طَطَّوْرَ إِغِيُواْيِ أَوُيَنْسُ، سُكَ تَڢِے وُرِنْ أَهَبْ سُكَثٜىٰ «بَاوَنْكَ بٜىٰنْهَدَدْ يَنَ ضُواْڧُواْ كَبَرْ شِ دَ رَيْ؞» سَيْ أَهَبْ يَثٜىٰ «أَشٜىٰ، يَنَدَ رَيْ؟ أَيْ، شِے طَنْعُوَنَنٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka sa tufafin makoki, suka ɗaura igiyoyi a wuyansu, suka tafi wurin Sarkin Isra'ila, suka ce, “Baranka, Ben-hadad, yana roƙonka ka bar shi da rai.” Ahab kuwa ya amsa ya ce, “Har yanzu yana da rai? Ai, shi kamar ɗan'uwana ne.”