1 Kings 20:39 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda sarki yake wucewa, sai annabin ya yi kira da ƙarfi gare shi ya ce “Ni bawanka na tafi yaƙi, sai ga wani ya kawo mini wani mutum, ya ce, ‘Ka riƙe wannan mutum, kada ka bar shi yă kuɓuta ko da ƙaƙa, idan ka bari ya kuɓuta, a bakin ranka, ko kuwa ka biya talanti ɗaya na azurfa.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ سَرْكِے يَذُواْ وُثٜىٰوَ سَيْ أَنَّبِنْ يَيِ كِرَا يَثٜىٰ «مَيْغِرْمَ، إِنَ ثِكِنْ يَاڧِنْ، سَيْ وَنِ سُواْجَ يَكَٰوُاْ وَنِ مُتُمِنْ دَ عَكَ كَامَ عَيَاڧِنْ يَثٜىٰ إِنْ لُورَ دَشِ؞ يَكُمَ ثٜىٰ عِدَنْ مُتُمِنْ يَغُدُ ذَاعَ سَا إِنْ بِيَ دَ رَيْنَ، كُواْ كُوَ ذَاعَ سَا إِنْبِيَ أَظُرْڢَا دُبُو عُكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da sarki yake wucewa, sai ya kira sarki, ya ce, “Ni baranka na tafi yaƙi, sai ga shi, soja ya kawo mini mutum, ya ce mini, ‘Ka riƙe wannan mutum, kada ka bar shi ya kuɓuta ko da ƙaƙa, idan ka bari ya kuɓuta a bakin ranka, ko kuwa ka biya talanti ɗaya na azurfa.’