1 Kings 20:40 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda bawanka yana fama, yana kai da kawowa, sai mutumin ya ɓace.” Sai sarkin Isra’ila ya ce, “Hukuncinka ke nan, ka furta shi da kanka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا يَايِنْ دَ وَطَنْسُ أَبُبُوَ سُكَ طَوْكِ حَنْكَلِنَ، سَيْ مُتُمِنْ يَغُدُ؞» سَرْكِے أَهَبْ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «دَ بَاكِنْكَ كَشَيْدَ لَيْڢِنْكَ، دُواْمِنْ حَكَ ذَاكَ كَرْٻِ حُكُنْثِنْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da na shiga fama da kai da kawowa sai mutumin ya tsere.” Sai Sarkin Isra'ila ya ce masa, “Haka shari'arka za ta zama, gama kai da kanka ka yanke shari'ar.”