1 Kings 20:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarkin Isra’ila ya tattara dukan dattawan ƙasar, ya ce musu, “Ku duba fa, wannan mutum yana neman tsokana! Sa’ad da ya aika in ba shi matana da ’ya’yana, azurfana da zinariyana, ban hana masa ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے أَهَبْ يَكِرَا دُكَنْ شُوغَبَنِّنْ ڧَسَرْ يَثٜىٰ مُسُ «كُغَ يَدَّ وَنَّنْ مُتُمِنْ يَكٜىٰ ڟُواْكَنَرْمُ! يَعَيْكَ مِنِ دَ سَڧُواْ إِنْ بَاشِ مَاتَانَ دَ یَیَنَدَ أَظُرْڢَاتَ دَ ظِينَارِيَاتَ، نِے كُوَ بَنْڧِ مَسَبَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ahab Sarkin Isra'ila kuwa ya kirawo dukan dattawan ƙasar, ya ce, “Ku gani fa, ku duba yadda mutumin nan yake neman rikici, gama ya aiko don in ba shi matana, da 'ya'yana, da azurfata, da zinariyata, ni kuwa ban hana masa ba.”