1 Kings 20:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka ya ba wa ’yan aikan Ben-Hadad amsa, ya ce, “Ku faɗa wa ranka yă daɗe, sarki, ‘Bawanka zai yi dukan abin da ka bukaci da farko, amma wannan na ƙarshe ba zan iya yin ba.’ ” Suka tafi suka kai amsar wa Ben-Hadad.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ أَهَبْ يَثٜىٰ وَ یَنْ عَيْكَ نَ بٜىٰنْهَدَدْ «كُڢَطَا وَ مَيْغِرْمَ سَرْكِے ثٜىٰوَ نَيَرْدَ دَ سَڧُواْ نَڢَرْكُوانْ، عَمَّا بَذَنْ عِيَيِنْ نَبِيُنْبَ؞» یَنْ عَيْكَ سُكَ تَڢِے سُكَسَاكٜىٰ دَاوُاْوَ دَ وَنِ سَڧُواْ
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya ce wa jakadun Ben-hadad, “Ku ce wa maigirma, sarki, dukan abin da ya nema a wurina da farko, zan yi, amma wannan na ƙarshe, ban zan iya yi ba.” Jakadun kuwa suka koma da wannan labari.