1 Kings 21:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma ku zaunar da waɗansu ’yan iska biyu ɗaura da shi, ku sa su ba da shaida cewa ya zagi Allah da sarki. Sa’an nan ku ɗauke shi ku jajjefe shi da dutse sai ya mutu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَسَا یَنْ إِسْكَ غُدَا بِيُ سُڢُسْكَنْثٜىٰشِ، سُيِ تَكَٰوُاْ هُجُّواْجِ عَكَنْسَ سُنَ ثٜىٰوَ ‹كَيْ كَلَعَنْثِ اللَّهْ دَ سَرْكِے؞› سَعَنً كُطَوْكٜىٰشِ كُجٜىٰجّٜىٰڢٜىٰشِ دَ دُوَڟُو حَرْ سَيْ يَمُتُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A kuma sa 'yan iska guda biyu, su yi ta zarginsa, su riƙa cewa, ‘Nabot ya zagi Allah da sarki.’ Sa'an nan ku tafi da shi, ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.”