1 Kings 21:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai dattawa da manyan gari, waɗanda suke zama a birnin da Nabot yake, suka yi kamar yadda Yezebel ta umarta a cikin wasiƙun da ta rubuta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مُتَنٜىٰنْ بِرْنِنْسَ دَ دَتَّاوَنْ تَرٜىٰدَ مَنْيَنْ مُتَنٜىٰنْ بِرْنِنْ سُكَيِ دَيْدَيْ كَمَرْ يَدَّ يٜىٰظٜىٰبٜىٰلْ تَرُبُوتَ عَيِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutanen birnin kuwa, dattawa da fādawan da suke zaune a birnin suka yi yadda Yezebel ta sa su yi, kamar yadda aka rubuta a wasiƙun da ta aika musu.