1 Kings 21:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan mai da gidanka kamar gida Yerobowam ɗan Nebat, da na Ba’asha ɗan Ahiya, domin ka tsokane ni har na yi fushi, ka kuma sa Isra’ila ya yi zunubi.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ ذَيْسَا غِدَنْكَ يَهَلَّكَ كَمَرْ غِدَنْ يٜىٰرُواْبُواْوَمْ طَنْ نٜىٰبَتْ دَ كُمَ غِدَنْ بَعَشَ طَنْ أَهِيَ، غَمَا كَا سَا يَهْوٜىٰهْ يَيِ ڢُشِے، كَكُمَ سَا مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَيِ ذُنُوبِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zan sa gidanka ya zama kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat, da gidan Ba'asha ɗan Ahija saboda ka sa ni in yi fushi, ka kuma sa mutanen Isra'ila suka yi zunubi.’