1 Kings 22:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zedekiya ɗan Kena’ana kuwa ya yi ƙahonin ƙarfe ya kuma furta, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan za ka tunkuyi Arameyawa har su hallaka.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً طَيَ عَثِكِنْسُ مَيْ سُونَ صَدِڧِيَ طَنْ كٜىٰنَعَنَ يَيِ وَكَنْسَ ڧَهُواْنِنْ بَڧِنْ ڧَرْڢٜىٰ يَثٜىٰ «إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ ، ‹دَ وَطَنَّنْ ڧَهُواْنِ ذَاكَ تُورَ سُرِيَاوَا حَرْ سُهَلَّكَ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zadakiya ɗan Kena'ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan ƙahoni za ka tunkuyi Suriyawa har su hallaka.’ ”