1 Kings 22:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Mikahiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji mai rai, zan faɗa masa kawai abin da Ubangiji ya faɗa mini.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا مِكَيَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «نَا ضَنْڟٜىٰ دَ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ مَيْ رَيْ، أَبِنْدَ يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ إِنْڢَطَا شِينٜىٰ كَطَيْ ذَنْ ڢَطَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji, abin da Ubangiji ya faɗa mini, shi ne zan faɗa.”