1 Kings 22:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da suka kai, sai sarki ya tambaye shi, ya ce, “Mikahiya, mu kai yaƙi a kan Ramot Gileyad, ko kada mu kai?” Ya amsa ya ce, “Yaƙe ta, za ka kuwa yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita cikin hannun sarki.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ يَذُواْ غَبَنْ سَرْكِے أَهَبْ، سَيْ سَرْكِے يَثٜىٰ مَسَ «مِكَيَ، مُڢِتَ مُڢَاطَوَ رَمُواتْ غِلٜىٰيَدْ دَ يَاڧِ كُواْ مُبَرِ؟» مِكَيَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «كَڢَاطَ مُسُ دَ يَاڧِ، أَيْ، ذَاكَثِ نَصَرَا؞ يَهْوٜىٰهْ ذَيْبَادَ عِتَ أَ حَنُّنْكَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu tafi Ramot don yaƙi, ko kuwa kada mu tafi?” Ya amsa masa ya ce, “Ka haura, za ka yi nasara, Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”