1 Kings 22:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Saboda haka yanzu Ubangiji ya sa ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawanka. Ubangiji ya zartar maka da masifa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مِكَيَ يَثٜىٰ «تُواْ، كَا غَنِ، يَهْوٜىٰهْ يَا سَا رُوحٌ ڧَضْيَا عَبَاكِنْ دُكَنْ أَنَّبَاوَنْكَ؞ غَمَا يَا رِغَا يَا ڢَطَا شِرِنْسَ نَمَسِيڢَ دُواْمِنْكَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mikaiya ya ce, “Ga abin da ya faru, Ubangiji ya bar annabawanka su faɗa maka ƙarya. Amma Ubangiji kansa ya riga ya zartar maka da masifa.”