1 Kings 22:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Zedekiya ɗan Kena’ana ya hau ya mari Mikahiya a fuska. Ya yi tambaya, “A wace hanya ce ruhu daga Ubangiji ya bar ni ya yi maka magana?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ أَنَّبِے صَدِڧِيَ طَنْ كٜىٰنَعَنَ يَتَڢِے وُرِنْ مِكَيَ يَبَا شِ مَرِ عَكُمَتُ سَيْ يَتَمْبَيٜىٰشِ يَثٜىٰ «تُنْ يَوْشٜىٰ نٜىٰ رُوحٌ يَهْوٜىٰهْ يَبَرْنِ يَذُواْ يَيِ مَغَنَ دَكَيْ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Zadakiya ɗan Kena'ana ya matso kusa ya mari Mikaiya a fuska, ya ce, “Ƙaƙa Ruhun Ubangiji ya bar ni, ya zo ya yi magana da kai?”