1 Kings 22:43 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A cikin kome ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa Asa, bai kuma kauce daga gare su ba; ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Amma bai rurrushe masujadai da suke kan tuddai ba, mutane kuwa suka ci gaba da miƙa hadayu suna kuma ƙone turare a can.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَيِ تَڢِيَ أَ حَنْيَ مَيْݣَوْ كَمَرْ بَابَنْسَ أَسَ، بَيْ كُمَ كَوْثٜىٰبَ؞ يَيِ أَبِنْدَ يَكٜىٰ دَيْدَيْ أَعِدُوانْ يَهْوٜىٰهْ ؞ عَمَّا دَيْ بَيْ كَوَرْدَ وَطَنْسُ وُرَارٜىٰنْ سُجَّدَ بَ، مُتَنٜىٰ سُكَ ثِيغَبَدَ مِيڧَ هَدَايُ سُنَ ڧُواْنَ تُرَارٜىٰ أَوُرَارٜىٰنْ سُجَّدَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya bi halin tsohonsa, Asa, bai karkace ba. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Duk da haka ba a rushe wuraren tsafin na tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu, suka ƙona turare a tuddan.