1 Kings 22:50 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yehoshafat kuwa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a birnin Dawuda kakansa. Sai Yehoram ɗansa ya gāje shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يٜىٰهُواْشَڢَتْ يَكُواْمَ غَ كَاكَنِّنْسَ، عَكَ بِنّٜىٰشِ تَرٜىٰدَسُو عَبِرْنِنْ دَاوُدَ؞ سَيْ طَنْسَ يٜىٰهُواْرَمْ يَغَاجٜىٰشِ يَذَمَ سَرْكِے؞ ﴿شٜىٰكَرَا 853-852 كَاڢِنْ حَيْڢُوَرْ عِيسَىٰ ﴾
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yehoshafat kuwa ya rasu, aka binne shi a inda aka binne kakanninsa a birnin kakansa Dawuda. Ɗansa Yehoram ya gaji sarautarsa.