1 Kings 3:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Solomon ya farka, ya gane ashe mafarki ne. Ya koma Urushalima, ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji ya miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama. Sa’an nan ya shirya wa fadawansa biki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ سُلَيْمَٰنُ يَڢَرْكَ سَيْ يَغَانٜىٰ أَشٜىٰ مَڢَرْكِ نٜىٰ؞ سَيْ يَتَڢِے عُرُوشَلِيمَ يَڟَيَ أَغَبَنْ عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْ يَهْوٜىٰهْ يَمِيڧَ هَدَايُ نَڧُواْنَاوَا دَ هَدَايُ نَڠَرَنْ زُمُنْثِ؞ سُلَيْمَٰنُ يَكُمَ شِرْيَ بِكِ دُواْمِنْ دَتَّاوَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Sulemanu ya farka, ashe, mafarki ne, Sa'an nan ya zo Urushalima, ya tafi ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Ya miƙa hadayu na ƙonawa, da hadayu na salama. Ya kuma yi wa dukan barorinsa biki.