1 Kings 3:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma ɗaya matar ta ce, “A’a! Mai rai ɗin ne ɗana; mataccen naki ne.” Amma ta farin ta nace, “A’a! Mataccen ne naki; mai ran ne nawa.” A haka suka yi ta gardama a gaban sarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ طَيَ مَثٜىٰنْ تَيِ مَغَنَ تَثٜىٰ «أَعَ، يَرُواْ مَيْ رَيْ نٜىٰ طَانَ، عَمَّا مَتَثّٜىٰنْ نٜىٰ طَنْكِ!» عَمَّا مَثٜىٰ نَڢَرْكُواْ تَثٜىٰ «أَعَ، مَتَثّٜىٰنْ يَرُوانْ نٜىٰ طَنْكِ؞ نَوَنٜىٰ مَيْ رَيْ!» سُكَيِ تَغَرْدَمَ أَغَبَنْ سَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma ɗaya matar ta ce, “A'a, mai ran shi ne nawa, mataccen kuwa shi ne naki!” Sai ta fari ta ce, “A'a, mataccen shi ne naki, mai rai ne nawa!” Haka suka yi ta gardama a gaban sarki.