1 Kings 3:26 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ainihin mamar ɗan da yake a raye ta cika da tausayi saboda ɗanta, sai ta ce wa sarki, “Ina roƙonka, ranka yă daɗe, kada ka kashe yaron! Ka ba ta kawai!” Amma ɗayan matar ta ce, “Kada a ba kowa daga cikinmu ɗan da rai, a ci gaba a raba shi!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَيْنِحِنْ مَثٜىٰنْ دَ يَرُوانْتَ نٜىٰ مَيْ رَيْ، تَايِ وَسَرْكِے كُوكَا دُواْمِنْ يَوَنْ ڧَوْنَ دَ تَوْسَيِنْ دَ تَكٜىٰدَشِ عَكَنْ طَنْتَ؞ تَاثٜىٰ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، كَدَ كَكَشٜىٰ يَرُوانْ! كَبَاتَ كَوَيْ!» عَمَّا طَيَنْ مَثٜىٰنْ تَثٜىٰ «كَدَ كُبَا وَنِنْمُ، أَ رَبَشِ كَشِ بِيُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda zuciyar mahaifiyar ta ainihi ta cika da juyayin ɗanta, ta ce wa sarki, “Ranka ya daɗe kada a kashe yaron! A ba ta!” Amma ɗayar ta ce, “Kada a ba kowa daga cikinmu, a ci gaba a raba shi.”