1 Kings 4:23 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
shanun da aka yi kiwo a gida guda goma, shanu ashirin da suka ƙoshi daga kiwo, tumaki da awaki ɗari; ban da ƙishimai, bareyi, batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ شَانُو غُواْمَ وَطَنْدَ عَكَيِ كِيوُانْسُ أَغِدَا دَ شَانُو عَشِرِنْ دَ عَكَيِ كِيوُانْسُ أَدَاجِ دَ تُمَكِ دَ أَوَكِ طَرِے، تَرٜىٰدَ بَرٜىٰوَ دَ غَدَ دَ نَامَنْ دَاجِ نَدَنْغِنْ بَرٜىٰوَ دَ ظَبُواْ مَاسُ ڧِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
da turkakkun bijimai goma, da shanu ashirin daga makiyaya, da tumaki ɗari banda kishimai, da bareyi, da batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.