1 Kings 4:33 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya yi magana a kan rayuwar itatuwa, daga al’ul na Lebanon zuwa hizzob da yake girma a bangaye. Ya kuma yi koyarwa game da dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kuma kifi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَيِ مَغَنَ غَمٜىٰدَ عِتَتُوَ دَغَ إِتَاثٜىٰنْ سٜىٰدَ دَيَكٜىٰ أَ لٜىٰبَنُوانْ ذُوَا ڟِرٜىٰ ڟِرٜىٰنْ إِظُوابْ دَسُكٜىٰ غِرْمَ عَكَنْ بَنْغُواْ؞ يَيِ مَغَنَ غَمٜىٰدَ دَبُّواْبِے دَ ڟُنْڟَيٜىٰ دَ دَنْغِنْ مَثِيظَيْ دَ ڧَدَنْغَرُ دَ كِيڢَيٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya yi magana a kan itatuwa da tsire-tsire tun daga itacen al'ul da yake a Lebanon har zuwa ɗaɗɗoya da take tsirowa a jikin bango. Ya kuma yi magana a kan dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kifaye.