1 Kings 5:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Hiram sarkin Taya ya ji an shafe Solomon sarki yă gāji mahaifinsa Dawuda, sai ya aika da jakadunsa zuwa wurin Solomon, gama shi da Dawuda abokai ne sosai dukan kwanakinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حِرَمْ سَرْكِنْ تَيَ كُوَ يَعَيْكَ دَ وَكِلَيْ سُغَيْ دَ سُلَيْمَٰنُ سَعَدَّ حِرَمْ يَجِ ثٜىٰوَ أَنَّطَ سُلَيْمَٰنُ سَرْكِے أَمَڟَيِنْ بَابَنْسَ دَاوُدَ، غَمَا شِے دَ دَاوُدَ أَبُواْكَيْ نٜىٰ سُواْسَيْ دُكَنْ ݣُونَكِنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Hiram, Sarkin Taya, ya aiki jakadunsa zuwa wurin Sulemanu, sa'ad da ya ji ya gāji tsohonsa, gama Hiram abokin Dawuda ne ƙwarai dukan kwanakinsa.