1 Kings 5:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ka san cewa saboda yaƙe-yaƙen da abokan gāba suka yi da mahaifina a kowane gefe, ya sa bai iya gina haikali domin Sunan Ubangiji Allahnsa ba, sai da Ubangiji ya sa abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كَا سَنْ ثٜىٰوَ دَاوُدَ بَابَنَ بَيْ غِنَا غِدَا دُواْمِنْ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْسَ بَ، سَبُواْدَ يَوَنْ يَاڧٜىٰ يَاڧٜىٰ دَ أَبُواْكَنْ غَابَنْسَ دَسُكٜىٰ كٜىٰوَيٜىٰ دَشِ؞ يَجِرَا سَيْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَبَا شِ نَصَرَا عَكَنْسُ، يَسَاسُ عَڧَرْڧَشِنْ ڧَڢَاڢُنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ka sani tsohona, Dawuda, bai iya gina Haikalin yin sujada ga Ubangiji Allahnsa ba saboda fama da yaƙe-yaƙe da maƙiyan da suke kewaye da shi, kafin Ubangiji ya mallakar masa da su.