1 Kings 6:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya kuma gina ɗakunan gefe duka a gefen haikalin. Tsayin kowanne, kamu biyar ne, aka haɗa su da haikalin da manyan katakan al’ul.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَغِنَ طَكُنَنْ سَمَنَّنْ كٜىٰوَيٜىٰ دَ غٜىٰڢٜىٰ عُكُ نَبَنْغُوانْ غِدَنْ، كُواْوَنٜىٰ هَوَ ڧَڢَا بَݣَويْ دَ رَبِے نٜىٰ؞ كَتَكَنْ بِمْ نَسٜىٰدَ نٜىٰ سُكَ حَطَ طَكُنَنْ دَ بَنْغُوانْ غِدَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Benayen da ya gina kewaye da Haikalin, kowane bene tsayinsa kamu biyar. An haɗa su da Haikalin da katakan itacen al'ul.