1 Kings 7:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Huram ya yi wani ƙaton kwano na ƙarfen tagulla, da ya kira Teku. Zurfin kwanon nan kamu bakwai da rabi, fāɗinsa kamu goma sha biyar, da’irarsa kuma kamu talatin ne.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ هُرَمْ يَيِ وَنِ ڧَتُوانْ ݣُونُواْ دُواْمِنْ عَ أَجِيٜىٰ ضُوَ نَڧَرْڢٜىٰنْ تَغُلَّ، وَنْدَ عَكٜىٰ كِرَنْسَ تٜىٰكُ؞ ظُرْڢِنْسَ ڧَڢَا بَݣَويْ دَ رَبِے، ڢَاطِنْسَ ڧَڢَا غُواْمَشَا بِيَرْ، إِغِيَ مَيْ ڧَڢَا أَرْبَعِنْ دَ بِيَرْ ذَاتَ كٜىٰوَيٜىٰ بَاكِنْ ݣُونُوانْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Huram kuma ya yi kewayayyiyar babbar kwatarniya ta zubi da tagulla. Faɗinta kamu goma ne, tsayinta kuwa kamu biyar, da'irarta kuma kamu talatin ne.