1 Kings 7:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A kewayen bakin ƙaton kwanon akwai layi biyu na siffofin goran ƙarfen tagulla, akwai gora shida cikin kowane ƙafa. An yi zubinsu haɗe da kwanon nan da kira Teku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكٜىٰوَيٜىٰنْ بَاكِنْ ڧَتُوانْ ݣُونُوانْ أَݣَويْ لَيِ بِيُ نَصِڢُّواْڢِنْ غُواْرَ نَڧَرْڢٜىٰنْ تَغُلَّ، أَݣَويْ غُواْرَ شِدَ ثِكِنْ كُواْوَنٜىٰ ڧَڢَا؞ أَنْ نَرْكٜىٰ ڧَرْڢٜىٰنْ تَغُلَّ، أَنْيِ ظُبِے نَصِڢُّواْڢِنْ غُواْرَنْ حَطٜىٰ دَ ڧَتُوانْ ݣُونُوانْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Akwai goruna kewaye da gefensa. Gora goma a kowane kamu ɗaya. Suka kewaye kwatarniya. Gorunan jeri biyu ne, an yi zubinsu haɗe da kwatarniyar.