1 Kings 7:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kaurin kwanon ya kai tafin hannu, kuma da’iransa ya yi kamar da’iran kwaf, kamar bi-ranar da ta buɗe. Wannan kwanon da aka kira Teku yakan ci garwa dubu biyu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غٜىٰڢٜىٰنْ ڧَتُوانْ ݣُونُوانْ، كَوْرِنْسَ إِنْثِ عُكُنٜىٰ، كُمَ ݣُونُوانْ يَنَ عِيَ طَوْكَرْ لِتَ دُبُو أَرْبَعِنْ نَضُوَ؞ بَاكِنْ ڧَتُوانْ ݣُونُوانْ كَمَرْ نَݣُوڢْ نٜىٰ كُواْ ڢُلَوَرْ دَ تَبُوطُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kaurin kwatarniya ya kai taƙin hannu guda. An yi gefenta kamar finjali, kamar kuma furen bi-rana. Takan ci garwa dubu biyu.