1 Kings 7:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya yi babban zaure mai ginshiƙai, tsawonsa kamu hamsin, fāɗinsa kuwa kamu talatin. A gabansa kuwa akwai shirayi, kuma a gaban wannan shirayi akwai ginshiƙai da kuma rufin da yake a shimfiɗe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُلَيْمَٰنُ يَكُمَ غِنَا ذَوْرٜىٰ مَيْ غِنْشِڧَيْ، ڟَوُانْسَ ڧَڢَا سَبَعِنْ دَ بِيَرْ، ڢَاطِنْسَ ڧَڢَا أَرْبَعِنْ دَ بِيَرْ؞ أَغَبَنْ ذَوْرٜىٰنْ أَݣَويْ ذَوْرٜىٰ مَيْ غِنْشِڧَيْ وَنْدَ أَنْرُڢٜىٰ سَمَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya yi babban shirayi mai ginshiƙai, tsawonsa kamu hamsin, faɗinsa kamu talatin. Akwai kuma wani shirayi mai ginshiƙai a gabansa.