1 Kings 7:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A fadar da zai zauna kuwa, wadda aka gina a can baya, ya yi ta da irin fasali guda. Solomon ya kuma yi wata fada kamar wannan zaure domin ’yar Fir’auna, wadda ya auro.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غِدَنْ دَ سُلَيْمَٰنُ يَكٜىٰ ذَمَ عَثِكِ، أَنْغِنَ شِ أَوَنِ ڢِيلِ عَبَايَنْ بَبَّنْ طَاكِنْ شَرِيعَرْ نٜىٰ؞ أَنْ كُوَ غِنَاشِ كَمَرْ يَدَّ عَكَ غِنَا بَبَّنْ طَاكِنْ شَرِيعَ؞ سُلَيْمَٰنُ يَكُمَ غِنَاوَا مَاتَرْسَ، یَرْ سَرْكِنْ مَصَرْ، غِدَا كَمَرْ بَبَّنْ طَاكِنْ شَرِيعَرْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya gina gidan da zai zauna a farfajiya na ciki, wajen shirayi. ya kuma gina wa matarsa, 'yar Fir'auna, gida irin wannan.