1 Kings 7:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dukan waɗannan gine-gine, daga waje zuwa babban fili, da kuma daga tushen zuwa rufin, an yi su da duwatsun da aka yanka, aka kuma gyara da zarto a fuskokinsu na ciki da waje.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَنْ غِنٜىٰ غِنٜىٰنَّنْ دَغَ تُوشٜىٰ حَرْ رُڢِنْ أَنْيِسُ دَ دُوَڟُو مَاسُ ݣَوْ دَ كُمَ ڟَادَ؞ دَ ڢَارِ أَنْيَيَّنْكَ دُووَڟُنْ دَيْدَيْ كَمَرْ يَدَّ عَكَ عَوْنَ، سَعَنً عَكَ ڠَغْڠَرَسُ غَبَ دَ بَايَ دَ زَرْتُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Aikin gine-ginen nan, an yi shi da duwatsu masu tamani tun daga tushen har zuwa rufin. Sai da aka auna duwatsun sa'an nan aka yanka su da zarto, ciki da baya daidai da juna.