1 Kings 8:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Yanzu, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari ka cika wa bawanka Dawuda mahaifina alkawaran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza sun yi hankali cikin dukan abubuwan da suke yi, don su yi tafiya a gabana kamar yadda ka yi.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَنْذُ يَا يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ، بَرِ كَثِكَ أَلْڧَوَرِنْدَ كَيِ وَبَاوَنْكَ بَابَنَ دَاوُدَ دَ كَثٜىٰمَسَ، ‹عِدَنْ یَیَنْكَ مَظَا ذَاسُ لُورَ دَ رَايُوَرْسُ، سُكُمَيِ تَڢِيَ تَرٜىٰدَنِ كَمَرْ يَدَّ كَيْ كَايِ، تُواْ، كُلُّمْ ذَاعَ سَامِ وَنِ دَغَ ثِكِنْ عِيَلِنْكَ دَ ذَيْ غَاجِ كُجٜىٰرَرْ مُلْكٍ إِسْرَٰٓءِيلَ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yanzu fa, ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ka cika wa bawanka Dawuda, tsohona, sauran abin da ka alkawarta masa, da ka ce, ‘Ba za ka rasa mutum a gabana wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai zuriyarka sun mai da hankali, sun yi tafiya a gabana kamar yadda kai ka yi.’