1 Kings 8:32 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
sai ka ji daga sama, ka kuma yi wani abu. Ka shari’anta tsakanin bayinka, ka hukunta mai laifi, ka mai da laifinsa a kansa, mai gaskiya kuma ka nuna shi marar laifi ne bisa ga gaskiyarsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَا يَهْوٜىٰهْ ، سَيْكَجِ دَغَ سَمَ، كَيِ شَرِيعَ، كَيَنْكٜىٰ وَبَايِنْكَ حُكُنْثِ؞ كَحُكُنْتَ مَيْ لَيْڢِے كَمَيْدَ لَيْڢِنْسَ عَكَنْسَ، مَيْ غَسْكِيَ كُمَ كَنُونَ شِے مَرَرْ لَيْڢِے نٜىٰ بِسَغَ غَسْكِيَرْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ya Ubangiji ka ji daga Sama, ka shara'anta bayinka, ka hukunta mai laifin, ka ɗora masa hakkinsa a kansa, amma ka kuɓutar da mara laifin, ka sāka masa bisa ga adalcinsa.