1 Kings 8:36 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
ka ji daga sama, ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace ta rayuwa, ka kuma aika da ruwan sama a ƙasar da ka ba wa mutanenka gādo.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْكَ جِيسُ دَغَ سَمَ؞ كَغَاڢَرْتَ ذُنُبَنْ بَايِنْكَ وَتُواْ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ، كَكُواْيَ مُسُ سُيِ تَڢِيَ أَ حَنْيَرْ رَايُوَا مَيْݣَوْ؞ سَعَنً يَا يَهْوٜىٰهْ ، كَعَيْكَ دَ ضُوً سَمَ عَڧَسَرْكَ دَ كَبَا مُتَنٜىٰنْكَ تَذَمَ مَلَّكَرْسُ تَغَادُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
sai ka ji daga Sama, ka gafarta zunuban sarki, da na jama'arka Isra'ila. Ka koya musu kyakkyawar hanyar da za su bi, ka sa a yi ruwan sama a ƙasarka wadda ka ba jama'arka gādo.