1 Kings 8:48 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
in sun juye gare ka da dukan zuciyarsu, da dukan ransu a ƙasar abokan gābansu waɗanda suka kwashe kamammu, suka yi addu’a gare ka, suka fuskanci wajen ƙasar da ka ba wa kakanninsu, waje birnin da ka zaɓa, da kuma haikalin da na gina domin Sunanka;
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ كُمَ سُكَ تُوبَ دَ دُكَنْ ذُوثِيَارْسُ دَ حَنْكَلِنْسُ عَڧَسَرْدَ سُكٜىٰ بَوْتَا، سُكَيِ مَكَ أَدُّعَ سُنَ ڢُسْكَنْتَرْ ڧَسَرْدَ كَبَا كَاكَنِّنْسُ دَ بِرْنِنْدَ كَذَاٻَا دَ كُمَ غِدَنْدَ نَغِنَ دُواْمِنْ أَغِرْمَمَ سُونَنْكَ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan sun komo gare ka da zuciya ɗaya, da dukan ransu a ƙasar abokan gabansu waɗanda suka kai su bauta, suka yi addu'a gare ka, suna fuskantar ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, da Haikalin da na gina saboda sunanka,