1 Kings 8:63 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Solomon ya miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, shanu dubu ashirin da biyu, tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan Isra’ilawa suka keɓe haikalin Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُلَيْمَٰنُ يَيِ هَدَايَ تَڠَرَنْ زُمُنْثِ دَ شَانُو دُبُو عَشِرِنْ دَ بِيُ دَ تُمَكِ دُبُو طَرِے دَ دُبُو عَشِرِنْ؞ تَهَكَ سَرْكِے دَ دُكَنْ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَ كٜىٰٻٜىٰ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sulemanu kuwa ya miƙa wa Ubangiji hadaya ta salama da bijimai dubu ashirin da dubu biyu (22,000) da tumaki dubu ɗari da dubu ashirin (120,000). Ta haka sarki da dukan mutanen Isra'ila suka keɓe Haikalin Ubangiji.